Jallikattu kaalai

in #photographs6 years ago

Screenshot_2017-01-22-18-18-15-1.png
Mutane biyu sun mutu lokacin wasan hawan kaho a India
Mutane biyu ne suka mutu, bayan da saniya ta soke su a lokacin wasan gargajiya na hawan kaho a jihar Tamil Nadu ta kasar India.
An dawo da wasannin gargajiyar na jallikattu da aka saba yi a lokacin girbi na watan Janairu ne, bayan da gwamnati ta shige gaba wajen ganin kotun kolin kasar ta dahe haramcin da ta yi wa wasannin.
Wasu jama'ar da suka taru sun sha kauracewa wasannin gargajiyar na jallikatu-- ba wai saboda batun azabtar da dabobin , da kuma hadarin da ke tattare da hakan bane, amma saboda suna son a sake halarta shi.
Sarrafa mafadatan shanun abu ne da aka dade ana yi a jihar ta Tamil Nadu, a matsayin wasannin gargajiya, da kuma wasu tsatsube-tsatsube lokacin girbi.
A shekarar 2018 ne kotun kolin India ta haramta wasan hawan hako, a karkashin dokar kasar hana azabtar da dabbobi.

Coin Marketplace

STEEM 0.24
TRX 0.12
JST 0.029
BTC 67756.95
ETH 3539.34
USDT 1.00
SBD 3.14